Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce jami’anta tare da sauran hukumomin tsaro sun ceto mutane 20 da ke shirin hidimar ƙasa NYSC, waɗanda aka yi garkuwa da su a Jihar Imo ranar 1 ga Oktoba 2026.
Rundunar ta ce an gudanar da aikin ceton ne ta hanyar amfani da bayanan sirri, inda aka samu nasarar kuɓutar da mutanen tare da kai su asibiti domin duba lafiyarsu.
A halin yanzu, rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike da ƙoƙarin kamo waɗanda ake zargi da aikata garkuwar.
- Dankwambo ya wakilci Shugaban Majalisar Dattawa a taron EITI na duniya
- NiMet ta lashe lambar yabo ta AfriGEO kan yanayi da gargaɗin farko
- ACF ta bukaci gwamnatin tarayya ta faɗi gaskiyar halin da tattalin arziki ke ciki
A wani lamari daban, ’yan sanda a Kaduna sun kashe wani da suka bayyana a matsayin ɗan fashi tare da kwato bindigar AK-47, harsasai biyu da kuma shanun da aka yi awon gaba da su.
Haka kuma, a Kaduna, jami’an tsaro sun kama wani da ake zargi da satar shanu, inda binciken da aka gudanar a gidansa ya kai ga gano bindigar AK-47.
A Katsina kuwa, rundunar ta ce jami’anta sun dakile harin ’yan bindiga kan matafiya a hanyar Kir-yoyi zuwa Dangani, inda aka kashe wani ɗan bindiga tare da kwato adda.
Rundunar ta kuma ce an kama wasu mutane biyu a Nasarawa bisa zargin hannu wajen satar kusan shanu 900 daga Kachia a Jihar Kaduna, yayin da aka kama wani mutum a Enugu da ake zargi da fashi da makami tare da kwato bindiga ƙirar gida da harsasai biyu.
A Delta, an kama mutane biyu bayan wani rikici da ya jikkata mutane biyu, yayin da aka kwato almakashi da ake zargin an yi amfani da shi wajen kai harin.
Haka kuma, a Nasarawa an kama wani mutum da ake zargi da kashe ƙaninsa da wuƙa yayin wani rikici, yayin da a Oyo aka kama jami’in tsaro da mai aikin tsafta biyu da ake bincike kan mutuwar wani mutum da aka samu da alamun rauni.
A Ogun kuma, ’yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da yin kamar jami’in ’yan sanda tare da karɓar Naira dubu 48 daga wani ɗan ƙasa bisa yaudara. Rundunar ta ce wanda ake zargin tsohon ɗan gidan yari ne.