Rundunar Sojojin Najeriya da ƙasar Bangladesh sun amince da ƙara zurfafa haɗin gwiwar tsaro domin ƙarfafa ƙwarewar sojoji, inganta ilimin aikin soja da kuma haɓaka dabarun gudanar da ayyukan tsaro.

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 8 ga Oktoba 2026, lokacin da ya karɓi Babban Jakadan Bangladesh a Najeriya, Miah Md Mainul Kabir, wanda ya kai masa ziyarar girmamawa a Hedikwatar Sojojin Najeriya da ke Abuja.

Laftanar Janar Shaibu ya ce Rundunar Sojojin Najeriya a shirye take ta yi musayar ƙwarewa da Bangladesh a fannonin yaƙi da ta’addanci, da yaƙi da tayar da ƙayar baya da kuma amfani da fasahar jiragen sama marasa matuƙa wajen ayyukan soji.

Ya kuma ce Najeriya na da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan jin kai da kula da mutanen da rikice-rikice suka raba da muhallansu, yana mai umartar sassan hedikwatar sojoji da abin ya shafa su tsara shirye-shiryen horo na haɗin gwiwa da sauran tsare-tsaren da za su ƙara wa Rundunar ƙwarewa.

A yayin ziyarar, Babban Hafsan Sojojin ya amince da kafa ƙungiyar tsofaffin ɗaliban National Defence College Bangladesh a Najeriya, domin haɗa jami’an sojin Najeriya da suka kammala manyan kwasa-kwasan dabarun tsaro a Bangladesh.

A nasa ɓangaren, Ambasada Mainul Kabir ya jajanta wa Rundunar Sojojin Najeriya bisa hatsarin jirgin soji da ya faru a Jihar Ondo, tare da yaba wa gudunmawar da jami’an Najeriya ke bayarwa a ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ambasadan ya bayyana cewa jami’an Najeriya 154 sun halarci kwasa-kwasan National Defence College na Bangladesh, yana mai ba da shawarar ƙara faɗaɗa musayar ilimi da ƙwarewa ta hanyar shirye-shiryen Foreign Service Academy da na sojoji domin ƙarfafa jagoranci da haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *