Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga hukumomin gargajiya a faɗin Najeriya da su riƙa rubuta tarihin masarautunsu domin kare shi daga gurɓacewa da kuma adana al’adunsu ga al’ummomi masu zuwa.
Sultan ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a Zariya ta Jihar Kaduna, yayin bikin ƙaddamar da littafin “Emirs of Zazzau: A Biographical Study from 1800–2025”, wanda aka shirya a wani ɓangare na bikin cika shekaru shida da naɗa Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.
Ya yaba wa Sarkin Zazzau bisa rubuta tarihin masarautar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kare asali, al’adu da gadon mutanen masarautar.
- ’Yan sanda sun ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su a Imo
- NiMet ta lashe lambar yabo ta AfriGEO kan yanayi da gargaɗin farko
Sultan ya ce sarakunan gargajiya su ne suka fi dacewa su rubuta tarihin al’ummominsu saboda suna da ilimi da bayanan da suka dace game da abubuwan da suka faru a baya.
Ya ce ya taɓa ƙalubalantar Sarkin Zazzau da ya yi koyi da shi wajen rubuta tarihin Daular Usmaniyya, yana mai cewa shi ma ya wallafa littafin “Sultans of Sokoto” shekaru da suka gabata.
Sultan ya kuma yi kira ga sauran masarautun Najeriya da su fara rubuta tarihin nasu, yana mai cewa ya kamata al’umma su san asalinsu, inda suka fito da kuma inda suke son zuwa, maimakon barin kafofin sada zumunta su riƙa yaɗa bayanan da ka iya gurbata tarihi.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yaba wa Sarkin Zazzau kan wannan yunƙuri, yana mai cewa littafin zai taimaka wajen adana tarihin masarautar.
Shi kuwa Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce an wallafa littafin ne saboda samun wasu bayanai da ya bayyana a matsayin karkatattu da rashin inganci game da tarihin masarautar.
Ya ce al’ummomin da suka kasa rubuta da adana tarihinsu na fuskantar barazanar rasa asalinsu, al’adunsu da alaƙarsu da al’ummomin da za su zo nan gaba.
Bikin ya samu halartar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, malamai, masana tarihi da ’yan Majalisar Masarautar Zazzau, da sauran manyan baki.