Jam’iyyar ADC, ta ce za ta tattara, tare da haɗawa da sanar da jama’a sakamakon da wakilanta suka samu daga rumfunan zaɓe yayin babban zaɓen shekarar 2027.
Jam’iyyar ta ce za ta gudanar da hakan ne tare da mutunta alhakin da doka ta ɗora wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, na bayyana sakamakon hukuma da sanar da waɗanda suka lashe zaɓe.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarain jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta mayar da martani ne kan gargaɗin Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, game da wallafa sakamakon zaɓe da wasu suka tattara ba tare da izinin hukumar ba.
- Najeriya da Bangladesh sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro
- An kashe mutum uku a hare-haren da aka kai filayen jiragen saman Saudiyya
ADC ta ce tana da ’yancin tattara tare da yaɗa bayanan sakamakon zaɓe, tana mai dogaro da tanadin ’yancin faɗar albarkacin baki da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar.
Jam’iyyar ta ce wakilanta za su rubuta sakamakon da aka samu a rumfunan zaɓe, tsarin jam’iyyar kuma zai tattara bayanan, sannan a sanar da jama’a alkaluman da aka tantance tare da bayyana tushen bayanan da kuma matsayin su.
Sai dai ADC ta ce ta amince cewa INEC ce ke da ikon doka na bayyana sakamakon hukuma da kuma ayyana waɗanda suka lashe zaɓe, amma a ra’ayinta wannan alhaki bai kawar da ’yancin ’yan ƙasa na tattara da yaɗa sakamakon da suka samu ba.