Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC-PCC, ya soki matakin Gwamnatin Tarayya na rage farashin man fetur a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30.

Kwamitin ya bayyana matakin a matsayin wani yunƙuri na siyasa, yana mai cewa bai kamata a takaita rage farashin man fetur zuwa wata guda ba.

Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ADC-PCC, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Martanin na zuwa ne bayan da Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙin Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta sayar da man fetur a farashi na asali ta gidajen man NNPC na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu safarar jama’a fifiko.

Sai dai Ologbondiyan ya ce matakin ba zai magance matsalolin tattalin arziƙin da ’yan Najeriya ke fuskanta ba, yana mai tambayar abin da zai faru bayan cikar kwanaki 30.

Ya kuma yaba wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, kan abin da ya bayyana a matsayin sukar manufofin tattalin arziƙin Gwamnatin Tarayya, musamman matakin cire tallafin man fetur.

ADC-PCC ta ce sanarwar rangwamen na kwanaki 30 ta nuna cewa akwai damar rage wa ’yan Najeriya nauyin tsadar man fetur, yayin da ta yi kira ga gwamnati da ta samar da tsare-tsare na dindindin maimakon matakan wucin gadi.

A nasa bayanin, Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya jaddada cewa rangwamen ba komawar tsarin tallafin man fetur ba ne, inda ya ce gwamnati za ta sayar da man a farashin da aka samo shi, musamman domin rage wa masu jigilar jama’a nauyin tsadar man fetur.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *