Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta ce ta kama mutane da dama bisa zargin aikata laifuka daban-daban, ciki har da sayar da jabun lambobin babura da kekunan hawa masu ƙafa uku, da kisan gilla da jikkata mutane, da kuma mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya fitar, rundunar ta ce ta kama mutane uku da ake zargi da ƙerawa da sayar da jabun lambobin babura da kekunan hawa masu ƙafa uku a Suleja.
Binciken ya gano cewa biyu daga cikin waɗanda ake zargin sun yi ikirarin cewa jami’an inshorar ababen hawa ne, inda ake zargin sun sayar da sama da lambobi 60 na bogi da ke ɗauke da sunayen jihohin Kaduna da Nasarawa.
- ADC ta ce za ta tattara tare da wallafa sakamakon zaɓe a 2027
- Rage farashin man fetur na kwanaki 30 ba zai magance matsalolin tattalin arziƙin da ’yan Najeriya ke fuskanta ba – ADC
Rundunar ta ce yayin binciken an kwato lambobin bogi 61, da kwamfutocin tafi-da-gidanka guda biyu, da injinan buga takardu guda biyu, da takardun inshora na bogi da kuma Naira 870,000 da ake zargin kuɗin da aka samu daga haramtacciyar sana’ar.
An kuma gano wasu sabbin lambobi 10 da aka buga da sunan Jihar Kano.
A wani lamari kuma, ’yan sanda sun kama mutane uku da ake zargi da haɗa baki wajen kisan wata mata mai shekaru 65, a ƙauyen Kokolo.
Rundunar ta ce babban wanda ake zargin, mai shekaru 35 daga Jihar Kebbi, ya bayyana cewa an ɗauke shi aiki ne bisa zarginsa da cewa yana da ikon gano mayu, domin ya kashe wasu tsofaffin mata uku da ake zargi da maita.
A cewar rundunar, wanda ake zargin ya kashe matar tare da jikkata wata mata kafin kama shi.
An ce wani daga cikin waɗanda ake zargin ya yi masa alkawarin filaye guda biyu da kuma auren ’yarsa idan ya kammala aikin.
Rundunar ta ce ana ci gaba da neman wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin wanda ya tsere.
Haka kuma, a Kontagora, ’yan sanda sun ce sun kuɓutar da wani direban babur na haya daga hannun wasu mutane bayan wani fasinja da ake zargi ya shafa masa wani ruwa a fuska yayin da yake kan hanya, lamarin da ya sa direban ya fara jin jiri.
Rundunar ta ce an kama wanda ake zargin, yayin da aka kai direban asibiti bayan ya suma.
A Suleja kuma, an kama wani mutum da ake zargi da mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba, inda aka gano wata bindiga ƙirar gida a ƙarƙashin gadonsa. Wanda ake zargin ya ce ya samo bindigar ne daga wani ginin da aka bari, da nufin sayar da ita.
Rundunar ta kuma ce ta kama wani mutum a Maitumbi da ake zargi da hannu wajen kai wa Babban Jami’in Tsaro na M.I. Wushishi Estate hari tare da jikkata shi a kai.
A wani samame kuma, ’yan sanda sun kwato motar Toyota Corolla da aka yi watsi da ita a hanyar Zuru, wadda ke ɗauke da buhunan tabar wiwi 11, buhunan chaff guda biyar da kuma kilogram biyar na wani sinadari da ake zargin methamphetamine ne.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike kan dukkan waɗanda aka kama da kayayyakin da aka kwato, tare da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Haka kuma ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama wasu da ake nema dangane da laifukan.