Ƙungiyar TUC reshen Babban Birnin Tarayya Abuja ta umarci ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da mambobinta da su yi watsi da umarnin Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC na shiga yajin aikin sai abinda hali ya yi, kan rikicin da ke tsakanin gwamnatin birnin tarayya da Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya.

NLC ta umarci ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da ke Abuja da su fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026, sabo da rikicin.

Sai dai a cikin wata sanarwa, majalisar TUC  reshen Abuja, ta ce ba a tuntube ta ba kafin bayar da umarnin, kuma ba ta cikin waɗanda suka yanke shawarar shiga yajin aikin.

Sanarwar ta ce, An bayar da umarnin ba tare da tuntubar majalisar TUC ta Abuja ko wata ƙungiya da ke ƙarƙashinta a birnin ba.

Majalisar ta ƙara da cewa TUC ta Abuja ba ta da hannu a wannan yajin aiki, don haka ta umarci ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da mambobinta da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum tare da zuwa wuraren aikinsu kamar yadda suka saba.

Haka kuma, ta yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na tsoratarwa ko tilasta wa mambobinta shiga yajin aikin, inda ta buƙaci duk wanda aka yi wa hakan da ya kai rahoto ga sakatariyar TUC ta Abuja.

Majalisar ta kuma umarci shugabannin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da su yi watsi da duk wani umarni na kafa kwamitocin tilasta bin umarnin yajin aikin, matuƙar umarnin bai fito daga shugabancin TUC na Abuja ba.

Ta buƙaci ma’aikata su kwantar da hankalinsu, su kiyaye doka tare da kasancewa cikin shiri, tana mai cewa shugabancinta ne zai fitar da ƙarin umarni idan yanayin ya sauya.

TUC ta ce tana damuwa da walwalar yara, malamai da sauran ma’aikata a birnin tarayya, tana mai jaddada cewa ya kamata a warware rikicin ta hanyar tattaunawa da bin ƙa’idojin da aka tsara na hulɗar ƙwadago.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *