Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutum huɗu da ake zargi da satar motoci, tare da ƙwato motoci uku a wasu samame da ta gudanar tsakanin ranakun 8 da 9 ga Oktoba, 2026.

Sanarwar da Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar 11 ga Oktoba, ta ce an samu nasarorin ne sakamakon ayyukan bincike da tattara bayanan sirri, tare da haɗin gwiwar al’umma.

A samamen farko, rundunar ta ƙwato wata motar Toyota Corolla kirar 2010, mai launin toka, bayan wani mutum daga unguwar Darmanawa ya kai ƙara cewa ya bai wa mutun, wanda aka fi sani da Dambu, motar domin ya sayar masa da ita, amma ya karkatar da ita zuwa wani wuri ba tare da izininsa ba.

Rundunar ta ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun gano motar a hannun wani, wanda ya ce ya saye ta kan naira miliyan 7.5. Ana ci gaba da bincike kan lamarin.

A wani samame kuma, ’yan sanda sun kama wasu masu shekaru 23 da shekaru 25, bisa zargin satar wata ƙaramar motar haya ta Toyota Hiace, mai lambar rajista NSR 261 XB, daga kasuwar Singer a Kano.

Haka kuma, jami’an rundunar sun kama wani mai shekaru 40 daga Potiskum ta Jihar Yobe, tare da ƙwato wata motar ɗaukar kaya kirar Mitsubishi Canter, mai lambar rajista BLF 365 XA. An kama shi ne a unguwar Kadawa, inda aka kai motar garejin wani mutum domin a sauya mata launi.

A cewar rundunar, wanda ake zargin ya amsa cewa ya sace motar ne daga wani gareji a Potiskum. Rundunar ’yan sandan Kano ta tuntubi takwararta ta Jihar Yobe domin ɗaukar matakan da suka dace da kuma gano mai motar na gaskiya.

Rundunar ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da ake ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a laifukan.

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen, tare da kira ga masu motoci da su ƙara kula da tsaron dukiyoyinsu, su miƙa su ga amintattun mutane kawai, sannan su sanya na’urorin kariya domin rage haɗarin sata.

Ya kuma buƙaci jama’a su riƙa kai rahoton motsin da ake zargi ko yunƙurin sayar da motoci a farashi mai rahusa fiye da yadda aka saba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *