Daruruwan masu zanga-zanga da ke goyon bayan jam’iyyun adawa a Indiya sun yi tattaki zuwa Kotun Ƙoli ta ƙasar a ranar Litinin, domin nuna adawa da cire miliyoyin sunaye daga rajistar masu zaɓe.
Masu zanga-zangar na neman shugaban Hukumar Zaɓe ta Indiya, Gyanesh Kumar, ya yi murabus bisa zargin cewa sauye-sauyen da aka yi wa rajistar masu zaɓe na iya amfanar jam’iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai mulki ƙarƙashin Firaminista Narendra Modi.
Rahotanni sun ce an cire sunaye sama da miliyan 130 daga rajistar masu zaɓe tun bayan fara aikin sake tantancewa a shekarar da ta gabata. Daga cikin waɗanda aka cire akwai mutane miliyan 28 da suka mutu, miliyan 63 da suka ƙaura, da kuma miliyan 30 waɗanda ba a iya gano inda suke ba.
- HSSI ta bukaci a kawo ƙarshen auren wuri, a kare haƙƙin ’yan mata
- ’Yan sandan Kano sun kama mutum huɗu, sun ƙwato motoci uku da aka sace
- Sojoji sun hallaka ’yan ta’addar ISWAP sama da 40 a Borno
A ƙarshen makon da ya gabata, ’yan sanda sun tsare dubban masu zanga-zanga, ciki har da wasu shugabannin ƙungiyar matasa mai suna Cockroach Janta Party (CJP). Jami’an tsaro sun kuma hana masu zanga-zangar wucewa zuwa wasu sassan tsakiyar birnin New Delhi.
Hukumar Zaɓe ta musanta zargin fifita wata jam’iyya, tana mai cewa mutanen da aka cire sunayensu bisa kuskure za su iya sake yin rajista.
Jam’iyyar BJP ta zargi jam’iyyun adawa da ƙoƙarin raunana dimokuraɗiyyar ƙasar ta hanyar ƙalubalantar sahihancin ayyukan zaɓe.
Jam’iyyun adawa sun nufi Kotun Ƙoli ne domin shigar da ƙara kan sauye-sauyen rajistar masu zaɓe, bayan Alkalin Alƙalai na ƙasar, Surya Kant, ya ƙi amincewa da buƙatarsu ta ganawa da shi, ya bayyana cewa tunda batun yana gaban kotu, tattaunawa a kai ba za ta dace da ƙa’idojin aikin shari’a ba, inda ya ba su shawarar su shigar da ƙara a hukumance.
Hukumomi sun rufe tashoshin jirgin ƙarƙashin ƙasa guda shida na tsawon sa’o’i 10, tare da takaita zirga-zirga a wasu hanyoyi sama da 20. An kuma jibge jami’an tsaro sanye da kayan yaƙi da tarzoma a tsakiyar birnin, yayin da aka kafa shingayen tsaro a muhimman hanyoyi.
A wani mataki na daban, ’yan sandan New Delhi sun sanar da cewa filin Jantar Mantar ba zai ci gaba da kasancewa wurin da aka amince da gudanar da zanga-zanga a hukumance ba, inda aka ware wasu sabbin wurare uku domin gudanar da irin waɗannan taruka.
Ministan Noma, Shivraj Singh Chouhan, ya zargi babbar jam’iyyar adawa ta Congress da amfani da zanga-zangar wajen ƙoƙarin kwace mulki, sai dai masu zanga-zangar sun ce suna kare haƙƙin masu zaɓe da kuma ’yancin cin gashin kan hukumomin ƙasar.
Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan jaridar The Indian Express ta ruwaito cewa mataimakan shugaban Hukumar Zaɓe guda biyu sun nuna damuwa a cikin hukumar kan sauye-sauyen rajistar masu zaɓe, hanyoyin yin rajista da kuma tsarin fasahar zamani da ake amfani da shi.
Jam’iyyun adawa sun kuma yi zargin cewa Musulmi da sauran ƙananan ƙungiyoyin addini da al’umma sun fi fuskantar cire sunayensu, saboda ana ganin ba za su goyi bayan jam’iyyar mai mulki ba. Sai dai Hukumar Zaɓe da jam’iyyar BJP sun musanta wannan zargi.
Ƙungiyar matasan da ke shiga zanga-zangar ta kuma gudanar da wasu gangami kan batutuwa da suka haɗa da ƙarancin kayayyakin more rayuwa a makarantun gwamnati da rashin ayyukan yi.
Wannan na daga cikin manyan ƙalubalen siyasa da Firaminista Narendra Modi da jam’iyyarsa ke fuskanta tun bayan shafe shekaru 12 a kan mulki.