’Yar takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar National Rescue Movement (NRM), Dr Esther Okereke, ta ce idan aka zaɓe ta a matsayin shugabar ƙasar Najeriya, jama’ar karkara za su ji tasirin shugabanci nagari.
Ta kuma yi alƙawarin ba da muhimmanci ga samar da muhimman ababen more rayuwa, ciki har da hanyoyi da layukan dogo.
Okereke ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya yi da ita a Abuja ranar Lahadi.
Ta ce burinta na neman shugabancin ƙasar ya samo asali ne daga fahimtar wahalhalun da talakawa ke fuskanta a kullum, inda ta ce tana amfani da hanyoyin da jama’a ke bi, tana zuwa kasuwannin su, tare da ziyartar cibiyoyin kiwon lafiya na al’umma, don haka tana fahimtar matsalolin da suke ciki.
- Sojoji sun hallaka ’yan ta’addar ISWAP sama da 40 a Borno
- HSSI ta bukaci a kawo ƙarshen auren wuri, a kare haƙƙin ’yan mata
- ’Yan sandan Kano sun kama mutum huɗu, sun ƙwato motoci uku da aka sace
Okereke ta bayyana cewa jam’iyyar NRM ta kafa ingantattun tsare-tsaren tafiyar da jam’iyya a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, da ƙananan hukumomi 774. Ta kuma ce jam’iyyar tana da tsarin wayar da kan masu zaɓe a rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar.
Dangane da ababen more rayuwa, ’yar takarar ta nuna damuwa kan lalacewar manyan hanyoyin da ke haɗa jihohi, tana mai cewa hakan na kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki tare da jefa rayukan matafiya cikin haɗari.
Ta ce wata tafiya da ta yi kwanan nan domin halartar jana’izar wani ɗan uwa ta sake nuna mata irin wahalhalun da jama’a ke sha sakamakon lalatattun hanyoyi.
Ta bayyana cewa samar da ingantattun hanyoyi a dukkan jihohin Najeriya abu ne mai yiwuwa, tana mai cewa ana iya faɗaɗa ayyukan raya ababen more rayuwa da ake gudanarwa a Abuja zuwa sauran sassan ƙasar.
Okereke ta kuma ce rashin kula da muhimman ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arzikin jama’a na sa wasu ’yan siyasa amfani da talauci wajen sayen ƙuri’u da ƙananan kyaututtuka. A cewarta, samar da hanyoyi masu kyau, wutar lantarki mai ɗorewa, gidaje da wadataccen abinci zai taimaka wajen kare mutuncin jama’a da hana ɗaukar matasa aikin daba na siyasa.
’Yar takarar ta buƙaci ’yan Najeriya su yi amfani da katin zaɓensu na dindindin (PVC) wajen riƙa neman bayani da ɗora shugabanni a kan alhakin ayyukansu, maimakon karɓar kuɗi domin su zaɓi wani ɗan takara. Sai dai ta shawarci jama’a cewa za su iya karɓar kayan da ’yan siyasa ke rabawa, amma su zaɓi bisa la’akari da gaskiya da riƙon amana.
Ta jaddada cewa neman shugabancinta ba batun jinsi ba ne, illa batun wakilcin jama’a da kuma yi musu hidima. Ta ce tana son zama shugabar da za ta riƙa amsa tambayoyin jama’a kan yadda ake amfani da dukiyoyin ƙasa, tare da zama muryarsu a wuraren yanke shawara.
Okereke ta ƙare da kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da ƙuri’unsu wajen neman shugabanci na amana, tana mai cewa burinta shi ne yi wa jama’a hidima da kuma taimakawa wajen farfaɗo da gina Najeriya.