Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), reshen Babban Birnin Tarayya (FCT), da Ƙungiyar Malaman Najeriya (NUT), reshen FCT, sun yi watsi da barazanar Ministan Abuja, Nyesom Wike, na aiwatar da dokar “ba aiki, ba albashi” ga ma’aikatan da suka shiga yajin aiki.

Shugaban NLC na FCT, Knabayi Adalo, da Sakatariyar NUT ta FCT, Margaret Jethro, ne suka bayyana matsayinsu a cikin sanarwa daban-daban da suka fitar wa mambobinsu ranar Lahadi.

A ranar Juma’a ne Wike ya umarci shugabannin ƙananan hukumomin FCT da su aiwatar da dokar “ba aiki, ba albashi” ga ma’aikatan da suka shiga yajin aikin da NLC ta fara ranar 7 ga Oktoba, sakamakon rashin warware saɓani tsakanin gwamnati da ƙungiyar malamai.

Ministan ya kuma umarci shugaban ma’aikatan gwamnati na FCT da shugabannin makarantun firamare da sakandare da su riƙa buɗe rajistar halartar aiki a kullum domin gano ma’aikatan da ba su halarci aiki ba.

Adalo ya buƙaci ma’aikata da malamai da abin ya shafa su yi watsi da barazanar, yana mai cewa yajin aiki wata hanya ce ta halastacciyar fafutukar neman haƙƙi idan an bi ƙa’idojin doka.

Ya yi nuni da Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, Dokar Ƙungiyoyin Ƙwadago da kuma yarjejeniyoyin Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO).

Dangane da hana albashi, Adalo ya yi iƙirarin cewa tanadin “ba aiki, ba albashi” da aka ambata a Sashe na 43 na dokar ƙwadago ya shafi yajin aikin da ya saɓa wa doka.

Ya kuma zargi gwamnatin FCT da haddasa rikicin ta hanyar rashin kula da wasu haƙƙoƙin malamai, ciki har da sharuddan ɗaga darajarsu da batun matsayin wasu daraktoci da dokar shekarun ritayar malamai ta 2022 ta shafa.

Shugaban NLC ya kuma yi iƙirarin cewa wasu hukunce-hukuncen Kotun Ƙwadago ta Ƙasa sun goyi bayan biyan albashi a wasu yanayi da suka shafi halastaccen yajin aiki.

Ya umarci mambobin ƙungiyar da su ƙi sanya hannu a rajistocin halartar aiki da aka buɗe yayin yajin aikin, yana zargin ana amfani da su ne domin hukunta ma’aikata.

Adalo ya buƙaci ma’aikatan da ake yi wa barazana, cin zarafi ko aika musu da takardun neman bayani kan rashin zuwa aiki da su kai rahoto tare da shaidu zuwa sakatariyar NLC ta FCT.

Ya kuma gargaɗi shugabannin makarantu da kada su tilasta wa malamai sanya hannu a rajistoci ko tura sunayensu domin hukunta su.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *