Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro, musayar bayanan sirri da haɗa dabarun yaƙi na fannoni daban-daban domin tunkarar ƙalubalen tsaro da ke ƙara sauyawa a ƙasar.
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, yayin gabatar da lacca ga waɗanda suka kammala kwas na 10/2026 a Kwalejin Yaƙi ta Sojin Ƙasa ta Najeriya da ke Abuja.
Shaibu ya ce shirin faɗaɗa rundunonin Sojin Ƙasa daga takwas zuwa 12 wani mataki ne na ƙarfafa ikon rundunar wajen tunkarar barazanar tsaro, faɗaɗa wuraren da take kula da su da kuma hanzarta kai ɗauki a sassa daban-daban na ƙasar.
- NLC da NUT sun yi watsi da barazanar Wike kan hana ma’aikatan FCT albashi
- Kekere-Ekun ta bukaci alƙalai su rungumi fasahar zamani domin hanzarta shari’o’i
- Ingantattun alkaluman tattalin arziki ba su rage talauci ba – Peter Obi
Ya jaddada cewa faɗaɗawar ba wai ƙara yawan rundunoni da sojoji kawai ba ne, illa gina runduna mai ƙwarewa, saurin daidaitawa da yanayi, shiri don yaƙi da juriya wajen tunkarar barazanar tsaro.
Babban hafsan ya ce nasarar wannan shiri za ta dogara ne da haɗa ƙwararrun ma’aikata, fasahar zamani, sahihan bayanan sirri, ingantattun kayan aiki da tsarin jagoranci mai inganci. Ya kuma buƙaci kwamandoji su rungumi sabbin dabarun yaƙi tare da kiyaye ƙwarewa, ladabi da bin doka domin ƙarfafa amincewar jama’a.
A nasa jawabin, tsohon Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, wanda ya gabatar da lacca mai taken “Cin Nasara a Yanayin Tsaro Mai Sarƙaƙiya: Sake Tsara Rundunar Sojin Ƙasa domin Ayyukan Yaƙi na Fannoni Daban-daban,” ya ce akwai buƙatar sauya tsarin rundunonin soji, dabarun aiki da koyarwar yaƙi domin tunkarar sabbin barazanar tsaro.
Monguno ya jaddada muhimmancin haɗa ƙarfin yaƙi na ƙasa, sama, sararin intanet da yaɗa bayanai. Ya ce fasahohin zamani, ciki har da jiragen sama marasa matuƙi, basirar na’ura da hanyoyin sadarwa na zamani, suna sauya yadda ake gudanar da ayyukan soji.
Ya kuma buƙaci a ci gaba da zuba jari a kirkire-kirkiren fasaha, haɗa bayanan sirri, gyaran hukumomi da horar da jami’an soji domin su iya gudanar da ayyukansu a yanayin tsaro mai sarkakiya.
Tun da farko, Kwamandan Kwalejin Yaƙi ta Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo Janar Umar Alkali, ya gode wa Babban Hafsan Sojin Ƙasar bisa goyon bayan da yake bai wa kwalejin wajen horar da kwamandoji da shugabannin soji.
Ya ce mahalarta kwas na 10/2026 sun samu horo mai zurfi da aka tsara domin inganta tunaninsu na nazari, tsara ayyukan soji da ƙwarewar jagoranci.
Laccar na daga cikin shirye-shiryen kammala kwas ɗin, tare da jaddada ƙudurin rundunar na horar da shugabannin soji masu ilimi, ƙwarewar fasaha da shirin tunkarar ƙalubalen tsaro na zamani.