Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kai agaji ga iyalan da ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa suka shafa a sassan ƙasar.

Majalisar ta kuma bukaci a gyara hanyoyin da suka lalace, dawo da hanyoyin shiga al’ummomin da ambaliyar ta ware, tare da tallafa wa manoman da suka rasa hanyoyin samun abin rayuwarsu.

Wannan mataki ya biyo bayan ƙudurin da majalisar ta amince da shi, sakamakon ƙudurorin gaggawa da suka yi nuni da irin barnar da ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa suka haddasa, musamman a jihohin Anambra, Ebonyi da Imo.

Haka kuma, majalisar ta umarci kwamitocin da abin ya shafa da su tantance al’ummomin da bala’in ya shafa, sannan su gabatar da rahotonsu da shawarwarin matakan da ya kamata a ɗauka cikin wata guda.

Majalisar ta bayyana alhini ga iyalan da suka rasa ’yan uwansu, gidajensu da hanyoyin samun abin rayuwa sakamakon waɗannan bala’o’i.

Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da matsa lamba domin ganin an kula da halin da waɗanda abin ya shafa suke ciki, tare da samar musu da tallafin da ya dace.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *