Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da shafin Ask AA, domin bai wa ’yan Najeriya damar yi masa tambayoyi kai tsaye kan manufofinsa, tarihin aikinsa a gwamnati da shirye-shiryensa na tafiyar da ƙasa.
Shafin zai fara aiki da ƙarfe 8:30 na daren Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, kuma kyauta ne.
Jama’a za su iya tambayoyi kan tattalin arziki, tsaro, fasaha, samar da ayyukan yi da hanyoyin rage tsadar rayuwa.
- Kotun Ta Ɗage Sauraron Shari’ar El-Rufai Zuwa Disamba
- CBN ya ce burin Najeriya shi ne rage hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10
Daraktan yaɗa manufofin kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku, Phrank Shaibu, ya ce an ƙirƙiri shafin ne domin sauƙaƙa sadarwa tsakanin ɗan takarar da masu zaɓe, tare da amfani da fasaha wajen tattauna matsalolin ƙasa.
Ya ce Atiku zai amsa tambayoyin da kansa, yayin da tawagarsa za ta taimaka wajen bayar da amsoshi.
An kuma shirya samar da hanyar amfani da shirin ta rediyo domin al’ummomin da ba su da damar shiga intanet su ma su shiga tattaunawar.
Atiku ya ce ya ƙaddamar da shirin ne saboda ya yi imanin cewa shugabanci tattaunawa ce tsakanin shugaba da jama’a.
Ya kuma bayyana cewa zai kira wasu daga cikin waɗanda suka aiko da tambayoyi tare da barin lambobin wayoyinsu, domin jin matsalolin da suke fuskanta kai tsaye.