Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya ce burin bankin shi ne rage hauhawar farashin kayayyaki zuwa ƙasa da kashi 10 cikin 100 a matsakaicin lokaci.
Cardoso ya bayyana hakan ne a taron gabatar da damar zuba jari a Najeriya, wanda aka gudanar a Bangkok, Thailand, yayin taron shekara-shekara na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya na shekarar 2026.
- INEC ta bai ’yan takara da aka cire daga jerin sunaye wa’adin zuwa 24 ga Oktoba
- Fani-Kayode ya ce Atiku ya goyi bayan ƙin biyan fanshon tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways
A wajen taron, Cardoso da Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, sun tattauna da masu zuba jari kan matakan da gwamnati ke ɗauka domin inganta tattalin arzikin Najeriya, musamman ta fuskar manufofin kuɗi, kasuwar canjin kuɗaɗen waje da tsarin hada-hadar kuɗi.
An kuma bayyana cewa shirin ƙara jarin bankunan Najeriya ya samu kusan naira tiriliyan 4.65.
Haka kuma, an gabatar da ayyukan zuba jari guda 65 da suka shafi wutar lantarki, sufuri, noma, masana’antu da fasaha.
Cardoso ya ce daidaita farashin kayayyaki da fayyace manufofin tattalin arziki na da muhimmanci wajen ƙarfafa amincewar masu zuba jari da jawo jarin da zai taimaka wa ci gaban tattalin arzikin ƙasar na dogon lokaci.