Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya ƙaddamar da sabuwar gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasa mai suna Sovereignty League, da nufin amfani da wasanni wajen haɗa kan al’umma da samar da damammaki ga matasa.
Gasar za ta ƙunshi ƙungiyoyi 20 da za su wakilci yankuna daban-daban na ƙasar, domin faɗaɗa damar samun ƙwallon ƙafa mai inganci fiye da manyan birane.
Haka kuma, shirin na da manufar inganta gasar zuwa matakin ƙwararru da kuma zuba jari a makomar wasanni.
- Atiku ya ƙaddamar da shafin tambayoyi kai tsaye daga ’yan Najeriya
- Nwabufo ya bayyana darussa biyar daga ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC
- Majalisar Dattawa ta bukaci agajin gaggawa ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa
Bisa bayanin fadar shugaban ƙasar, ana sa ran ’yan wasan da aka zaɓa za su riƙa samun albashin kusan dala 300 a kowane wata, baya ga wasu alawus-alawus da sauran abubuwan more rayuwa.
Fadar shugaban ƙasar ta ce shirin zai taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi guda 1,000 tare da buɗe ƙofofin samun dama ga matasa a sassan ƙasar.
Wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnonin yankuna za su taka muhimmiyar rawa wajen tsara yadda za a gudanar da gasar.
Sai dai masu sharhi kan harkokin wasanni sun ce har yanzu ba a bayyana yadda sabon tsarin zai yi aiki tare da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Burkina Faso ba, wadda dokokin hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, suka ba kariya ta musamman.
Ƙaddamar da gasar yaa zo ne kwanaki kaɗan bayan da Traoré ya yi barazanar karɓe ragamar hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar, sakamakon rashin nasarar da Burkina Faso ta yi da ci 7-0 a wasan sada zumunta da Argentina.