Rundunar Sojin Najeriya ta gudanar da horo na kwanaki biyar ga manyan ƙananan hafsoshin runduna ta 8 da sashen Operation FANSAN YAMMA, domin ƙara musu ƙwarewa wajen jagorantar sojoji da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Babban Kwamandan runduna ta 8 kuma shugaban sashen Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar Bemgba Koughna, wanda Shugaban Ma’aikatan rundunar, Birgediya Janar Ibrahim Gambari, ya wakilta, ya yi maraba da mahalarta horon tare da godiya ga Cibiyar Bunƙasa Ƙwarewar Sojoji ta Najeriya bisa shirya shirin.
Koughna ya ce horon ya dace da manufar Babban Hafsan Sojin Najeriya ta gina runduna mai ƙwarewa, juriya da shirin tunkarar yaƙi, wadda za ta iya sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
- Majalisar Dattawa ta bukaci agajin gaggawa ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa
- Saudiyya ta ce ta lalata makami mai linzami a yankin Madina
- Gwamnan Zamfara ya bayyana matsayin APC gabanin zaɓen 2027
Ya bayyana cewa an tsara horon ne domin taimaka wa hafsoshin su fahimci nauyin da ke kansu, su inganta yadda suke jagorantar sojoji da kuma cike gibin da ake samu wajen gudanar da ayyukan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.
Ya kuma gargaɗe su kan yin amfani da kafafen sada zumunta ba bisa ƙa’ida ba.
A nasa jawabin, Darakta-Janar na Cibiyar Bunƙasa Ƙwarewar Sojoji ta Najeriya, Manjo Janar James Gwaza Khalifa Myam mai ritaya, wanda Manjo Janar Ifiok Obot mai ritaya ya wakilta, ya ce horon ya mayar da hankali ne kan jagoranci a fagen yaƙi, wanda ke buƙatar ladabi, ƙwarewa da jajircewa daga hafsoshi.
Ya ƙara da cewa shirin zai taimaka wajen bunƙasa basirar warware matsaloli, tunani mai zurfi da iya fahimtar halayen mutane, domin bai wa jami’an tsaro damar fuskantar sababbin ƙalubalen tsaro.
Darussan sun haɗa da yadda ake jagoranci, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, sarrafa motsin rai, tunani mai zurfi, illolin amfani da kafafen sada zumunta ba daidai ba, jagoranci a lokacin rikici da yaƙi, da kuma dokokin da ke jagorantar ayyukan sojoji.
Masu gabatar da darussan sun haɗa da Manjo Janar Ifiok Obot mai ritaya, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman mai ritaya, Farfesa Okey Ikechukwu, Misis Temitope Aiyedogbon da Kanal Cyril Oforumazi.