A wani rahoto da kakakin rundunar, CSP Ani Iniedu, ya fitar ranar 16 ga Oktoba, 2026, rundunar ta bayyana cewa a Jihar Oyo, jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar masu satar motocin alfarma a kan hanyar Oyo zuwa Ibadan.
An kuma ƙwato wata baƙar motar Lexus 350 SUV da aka sace, yayin da bayanan waɗanda aka kama suka taimaka wajen kama wasu mutane biyu da ake zargi da karɓar motocin a Jihar Legas.
- Wike ya buƙaci a sauya siyasar neman gata zuwa siyasar ɗaukar nauyi
- NiMet da TomorrowNow sun haɗa kai don inganta hasashen yanayi ga manoman Najeriya
- Rundunar sojin saman Najeriya ta gana da al’ummar Igbokoda kan aikin gano tarkacen jirgin sama
A Jihar Ebonyi, ’yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da hawa babur da ba shi da rajista kuma ake zargin sata aka yi, sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar gida guda biyu, alburusai 11 da wayar Android.
A wani lamarin daban a jihar, an kama wani mutum mai shekara 35 bisa zargin lalata da yarinya mai shekara 11, rundunar ta ce an kai yarinyar asibiti domin duba lafiyarta, kuma an tabbatar da cewa tana cikin kwanciyar hankali.
A Jihar Rivers kuwa, an kama wani mutum bayan rahoton zargin kai hari, da barazana ga rayuwa da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, binciken da aka gudanar a gidansa ya kai ga gano alburusai 20 na bindigar AK-47, adda guda da bindiga ta wasan yara.
A Jihar Nasarawa, jami’an tsaro sun kama wani mutum bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, tare da ƙwato bindiga ƙirar gida guda a New Nyanya, rundunar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama wani mutum da ya tsere da kuma gano alburusai.
A Jihar Adamawa kuwa, jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun fafata da waɗanda ake zargin ’yan Boko Haram ne bayan harin da suka kai ƙauyen Zangula da ke ƙaramar hukumar Gombi, an ce an killace yankin domin shawo kan barazanar tsaro da hana ƙarin asarar rayuka da dukiyoyi.
A Jihar Neja, jami’an ’yan sanda na musamman, da Hukumar DSS, da mafarauta da ’yan banga sun shiga aikin ceto mutanen da ’yan bindiga suka sace a kan hanyar Bangi, inda rundunar ta ce ana ci gaba da sintiri da binciken dazuzzuka domin kuɓutar da waɗanda aka sace ba tare da sun samu rauni ba, tare da kama maharan.
A Jihar Zamfara kuma, jami’an tsaro sun fara aikin ceto mutane uku da aka sace a wajen garin Daki Takwas bayan waɗanda suka sace su sun tsere kafin isowar jami’an tsaro.
A wani harin daban a Zamfara, jami’an tsaro sun kai ɗauki bayan ’yan bindiga sun kai hari kan matafiya a hanyar Kurar Mota, inda mutane uku suka samu raunukan harbin bindiga, tuni an kai su asibiti, inda aka tabbatar da cewa suna cikin kwanciyar hankali kuma an kwantar da su domin jinya.
A Jihar Ogun kuwa, ’yan sanda sun fara binciken mutuwar wani mutum da ya samu munanan raunuka a wani lamari da aka fara kai rahotonsa a matsayin haɗari, an ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar gawa na Babban Asibitin Jiha da ke Ota domin adanawa da gudanar da binciken gawar don gano ko akwai laifi a lamarin.
Rundunar ta ce sassan binciken manyan laifuka na jihohin da abin ya shafa ne ke gudanar da bincike kan al’amuran, ciki har da sassan Ibadan, Abakaliki, Fatakwal, Lafia, Yola, Minna, Gusau da Abeokuta.