Oyebanji, wanda ya fara mulkinsa a ranar 16 ga Oktoba, 2022, ya samu nasarar sake zaɓensa a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 20 ga Yuni, 2026. Sakamakon zaɓen da aka ruwaito ya nuna cewa ya samu ƙuri’u 319,224, yayin da babban abokin hamayyarsa, Wole Oluyede na jam’iyyar PDP, ya samu ƙuri’u 40,543.
Nasarar ta zo ne a lokacin siyasar gwamnan jihar ta kasance mai sauye-sauye, inda babu wani gwamna da ya taɓa samun wa’adi na biyu a jere tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
- Uzodimma ya jaddada muhimmancin ƙananan hukumomi wajen ci gaban ƙasa
- Shettima ya isa Ekiti domin wakiltar Tinubu wajen rantsar da Oyebanji
- Jirgin sama yayi saukar gaggawa a Abuja bayan kofarsa ta bude a sararin samaniya
Hakan ya ba Oyebanji damar ci gaba da jagorantar jihar tare da ƙoƙarin kammala manufofin da ya fara a wa’adinsa na farko.
An haifi Oyebanji a ranar 21 ga Disamba, 1967, a garin Ikogosi-Ekiti, ya karanci tarihi a Jami’ar Jihar Ondo, wadda yanzu ake kira Jami’ar Jihar Ekiti, inda ya kammala digirinsa na farko a shekarar 1989.
Daga bisani, ya samu digiri na biyu a fannin kimiyyar siyasa daga Jami’ar Ibadan a shekarar 1992, kafin zama gwamna, ya yi ayyuka daban-daban a fannin koyarwa, harkokin banki da siyasa.

Kafin ya hau kujerar gwamna, Oyebanji ya riƙe muƙamai daban-daban a gwamnatin Ekiti, ciki har da sakataren gwamnatin jihar a lokacin mulkin tsohon gwamna Kayode Fayemi, waɗannan ayyuka sun ba shi damar shiga harkokin gudanar da gwamnati tun kafin ya zama babban jagoran jihar.
A wa’adinsa na farko, gwamnatinsa ta mayar da hankali kan bunƙasa ababen more rayuwa, noma, ilimi da lafiya.
Daga cikin ayyukan da aka danganta da gwamnatinsa akwai bunƙasa filin jirgin saman Ekiti Agro-Allied International Cargo Airport, da kuma shirye-shiryen tallafa wa manoma da inganta wasu makarantu da cibiyoyin lafiya.
Yanzu da ya fara wa’adinsa na biyu, babban abin da ake sa ran shi ne yadda zai ci gaba da waɗannan shirye-shirye, samar da ƙarin ayyukan yi, inganta tsaro da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Nasarar sake zaɓensa ta ba shi damar ci gaba da mulki, amma yadda jama’a za su amfana da ayyukan gwamnatinsa ne zai kasance muhimmin ma’auni na wa’adinsa na biyu.