A ranar Abinci ta Duniya, mun yi nazari kan muhimman matakai biyar da ya kamata a ɗauka domin ƙara samar da abinci, da rage yunwa da inganta wadatar abinci a Najeriya, musamman ta fuskar noma da kiwo.

TAO Junction | Fraud Alert: Imposters Target Farmers In Jigawa State

1. Samar da ingantattun iri da kayan aikin noma

Gwamnati ta ƙara taimaka wa manoma wajen samun ingantattun iri, takin zamani, kayan aikin noma da horo kan hanyoyin noma na zamani domin ƙara yawan amfanin gona.

FG hands over 12 additional rehabilitated Irrigation schemes to Kano farmers – The Sun Nigeria

2. Bunƙasa ban-ruwa da inganta amfani da ƙasa

A faɗaɗa hanyoyin ban-ruwa domin manoma su riƙa noma a lokacin rani, tare da inganta sarrafa ƙasa da ruwa don samun amfanin gona a yanayi daban-daban.

Touring Vegetable Farming Impact in Kano, Nigeria - East-West Seed Knowledge Transfer

3. Ƙara tallafin kuɗi da horo ga manoma

A sauƙaƙa wa manoma samun rance mai sauƙin biya da sauran tallafin da za su taimaka musu wajen sayen kayan noma, sannan a ƙarfafa horas da su kan dabarun noma masu inganci.

Nexus24 Agrik | Sustainable Agricultural Supply Chains in Nigeria

4. Inganta adana amfanin gona da rage ɓarna

A gina ko inganta rumbunan ajiya, wuraren sarrafa amfanin gona da hanyoyin jigila domin rage lalacewar hatsi, kayan lambu da sauran kayan abinci bayan girbi.

Rice–Fish Farming Boosts Incomes, Food… | Sustainable Stories Africa

5. Bunƙasa noma, kiwo da kamun kifi cikin ɗorewa

A ƙarfafa noman hatsi, kayan lambu, kiwon dabbobi da kifaye, tare da amfani da fasahohi masu kare muhalli. Hakan zai taimaka wajen ƙara nau’o’in abinci da samar da ingantacciyar hanyar samun kuɗin shiga ga manoma da sauran masu samar da abinci.

Taken ranar abinci ta Duniya ta 2026; shi ne “Ƙirƙira a yau, ciyarwa gobe” wato (Innovate Today, Nourish Tomorrow), bisa bayanin Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO).

Taken ya jaddada muhimmancin amfani da fasaha da sabbin dabaru wajen samar da abinci da tabbatar da wadatarsa a nan gaba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *