Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, yayin taron shekara-shekara na Ƙungiyar Masu Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR), reshen Jihar Kano, wanda aka gudanar a Tahir Guest Palace da ke Kano.
Taron, wanda taken sa shi ne “Gudanar da Sakamakon Zaɓe: Rawar Jami’an Yaɗa Labarai”, ya tattauna muhimmancin sahihanci da ƙwarewa wajen sanar da sakamakon zaɓe.
- Dan’iya ya bukaci Tinubu ya sake duba nadin ɗan’uwan gwamnan Sokoto a INEC
- Kwastam ta kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 400, ta kai wa NDLEA
Bakori ya ce zaɓe ba abu ne da ke faruwa a rana ɗaya kawai ba, illa dai tsari ne da bayanai ke taka muhimmiyar rawa a cikinsa.
Ya bayyana cewa rashin kula da bayanai na iya haifar da jita-jita, tayar da hankali da kuma rage amincewar jama’a, yayin da ingantaccen yaɗa bayanai ke ƙarfafa zaman lafiya da dimokuraɗiyya.
Ya kuma ce jami’an yaɗa labarai na da alhakin kare gaskiya da yaƙi da labaran ƙarya, musamman yayin da ake jiran tattarawa ko sanar da sakamakon zaɓe.
Kwamishinan ya ce rundunar ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da kuma shirye-shiryen horarwa da wayar da kai ga ƙungiyoyin matasa, ’yan siyasa da masu aikin jarida.
Ya ƙara da cewa za ta ci gaba da ayyukan leƙen asiri da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin dakile kalaman ƙiyayya, daba ta siyasa da yaɗa bayanan ƙarya da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya.
A nasa jawabin, Babban Jami’in Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Kano, Ambasada Zango Abdu, ya tabbatar da shirin hukumar na gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci, gaskiya da bayyana gaskiya a 2027, ta hanyar inganta amfani da fasaha da ƙarfafa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki.
Taron ya samu halartar manyan baki, ciki har da Farfesa Sule Yau Sule da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Alhaji Mustafa Mohammed, ya wakilta.
Mahalarta sun jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, INEC, gwamnati da kafafen yaɗa labarai domin tabbatar da zaman lafiya a zaɓen 2027.