Dan’iya ya kuma bukaci Majalisar Dattawa ta gudanar da cikakken bincike kafin tabbatar da nadin, yana mai cewa an bayyana Farfesa Mustapha Aliu a matsayin ɗan’uwan Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, ta ɓangaren uwa, lamarin da ya ce ya sa ya zama dole a tabbatar da cancantarsa da ’yancinsa daga tasirin siyasa.
A cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Aminu Abdullahi, ya sanya wa hannu, Dan’iya ya jaddada cewa alaƙar iyali kaɗai ba ta isa ta zama hujjar hana mutum naɗin ba, sai dai ya ce ya kamata a binciki duk wata damuwa kan alaƙar siyasa da kuma ikon wanda aka naɗa na gudanar da aiki ba tare da nuna son kai ba.
- Mataimakin gwamnan Kano ya taya Oyebanji murnar komawa wa’adi na biyu
- Babban hafsan sojoji ya duba aikin gina barikin Bola Tinubu
Dan’iya ya yi nuni da sashe na 156(1)(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ya tanadi cewa mamba a INEC bai kamata ya kasance ɗan wata jam’iyyar siyasa ba, inda bukaci majalisar dattawa ta tantance ko Farfesa Aliu ya cika wannan sharadi da sauran ƙa’idojin da suka shafi naɗin.
Ya ce ’yancin INEC yana da matuƙar muhimmanci ga amincewar jama’a da sahihancin zaɓe, don haka bai kamata a ɗauki naɗin kwamishinonin hukumar a matsayin wani al’amari na siyasa kawai ba.
Ya kuma yi kira ga Sanatocin Sokoto da na Arewa maso Yamma, da sauran wakilan yankin, da su nemi cikakken bayani kan cancantar wanda aka naɗa.
Dan’iya ya ƙara da cewa idan bincike ya tabbatar da cewa wanda aka naɗa bai cika sharuddan kundin tsarin mulki ba, ya kamata Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da nadin, Shugaban Ƙasa kuma ya gabatar da wani wanda ya cancanta.
Ya ce kare martabar tsarin zaɓe da tabbatar da amincewar jama’a ya kamata su fi duk wata alaƙar siyasa muhimmanci.