Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, a Kwalejin Horar da Jami’an Kwastam da ke Ikeja, Legas, yayin bikin buɗe horon sababbin jami’an.
Mataimakin Kwanturol Janar mai kula da horo da tsare-tsare, Suleiman Chiroma, ne ya wakilce shi a wajen taron.
Ya ce hukumar ta himmatu wajen samar da ƙwararrun jami’ai masu ladabi da sanin ya kamata ta hanyar ingantaccen horo da samar da kayan aiki masu kyau.
- Babban hafsan sojoji ya duba aikin gina barikin Bola Tinubu
- Mataimakin gwamnan Kano ya taya Oyebanji murnar komawa wa’adi na biyu
A cewarsa, an zaɓi sababbin jami’an ne bayan sun yi nasara a gwaje-gwaje masu tsauri, bisa la’akari da damar da suke da ita ta bayar da gudunmawa wajen kare Najeriya da inganta ci gabanta.
Adeniyi ya bayyana cewa hukumar na sa ran jami’an za su yi aiki tukuru tare da samar da ingantaccen hidima ga al’umma, yana mai cewa za a horar da su domin su taka rawa wajen farfaɗo da tattalin arziki, bunƙasa ƙasa da wadata.
Ya kuma duba tare da yaba wa ci gaban da aka samu a kwalejin, musamman a wuraren wasanni, asibitin kwalejin da filin fareti, da kuma gyare-gyaren dakunan kwanan dalibai, bandakuna, ɗakin girki da azuzuwa.
Tun da farko, kwamandan kwalejin, Mataimakiyar Kwanturol, Patience Ita, ta bukaci sababbin jami’an da su kiyaye kyawawan ɗabi’u da gaskiya, tana mai cewa tana da yakinin za su saba da buƙatun shirin horon yayin da yake ci gaba.