Garo ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya fitar, inda ya ce ya wakilci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a bikin rantsar da Oyebanji.
Ya ce sake zaɓen Oyebanji na nuna irin amincewar da al’ummar Jihar Ekiti suka nuna wa shugabancinsa.
- Hukumar Shige da Fice ta horas da jami’ai 87 kan fasahar kula da iyakokin Najeriya
- Kotu ta yanke wa ’yan daba takwas hukuncin ɗaurin shekara takwas a Bauchi
Mataimakin gwamnan Kano ya kuma yi wa Oyebanji da mataimakiyarsa, Monisade Afuye, fatan samun nasarar gudanar da wa’adinsu na biyu, tare da samun ci gaba, shugabanci mai bai wa kowa dama da kuma ingantaccen ci gaba mai ɗorewa a jihar.
Garo ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa, bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar ’yan Najeriya.