Wata kotu a Jihar Bauchi ta yanke wa mutane takwas hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari kowannensu, tare da zaɓin biyan tarar naira 370,000, bisa laifin daba da tayar da hankalin jama’a a Unguwar Dim da ke cikin birnin Bauchi.
Rundunar ’yan sandan jihar ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne bayan samun ƙorafi daga kwamitin zaman lafiya da tsaro na Unguwar Dim a ranar 14 ga Oktoba, 2026, kan sake bullar ayyukan daba a yankin.
Sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar 17 ga Oktoba, ta ce jami’an rundunar yaƙi da manyan laifuffuka, tare da tawagar sintiri ta sashen ’yan sanda na “D” da mambobin kwamitin, sun kai samame maboyar waɗanda ake zargin a safiyar ranar 15 ga Oktoba.
- Hukumar Shige da Fice ta horas da jami’ai 87 kan fasahar kula da iyakokin Najeriya
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyu, sun ƙwato bindigogi AK-47 huɗu a Sokoto
A yayin samamen, jami’an tsaro sun kama mutum tara tare da ƙwato makamai da suka haɗa da sanduna, adduna, wuƙaƙe da wasu abubuwa masu haɗari, da kuma wasu abubuwan da ba a halatta amfani da su ba. Bayan kammala bincike, an gurfanar da mutum takwas a gaban kotu.
Rundunar ta ce dukkan waɗanda aka gurfanar sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi. Bisa hakan, kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru takwas kowannensu, tare da zaɓin biyan tarar naira 370,000 ga kowane mutum.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi maraba da hukuncin, yana mai cewa hakan ya nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da al’umma wajen yaƙi da laifuffuka.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da nufin kawar da daba, tada hankalin jama’a da sauran laifuffukan tashin hankali a jihar.