A Sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar 16 ga Oktoba, 2026, ta ce dakarun sun gudanar da samame ne a ranar 15 ga Oktoba.
Sanarwar ta ce dakarun Sashi na Biyu sun yi arangama da ’yan ta’adda a Dajin Waria, inda suka kashe ɗaya daga cikinsu tare da ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu da babura biyu, da wasu kayayyaki.
- Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance sabbin jami’an INEC gabanin zaɓe
- An tabbatar da mutuwar direban kungiyar Crown FC, yayin da ‘yan wasa da jami’ai suka jikkata a wani hatsarin mota
A wani samame da suka gudanar a ƙauyen Sarma, dakarun sun sake fafatawa da wani rukuni na ’yan ta’adda, inda suka kashe ɗaya daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere suka bar kayayyakinsu a wurin.
Bayan ci gaba da binciken yankin, dakarun sun ƙwato wasu babura shida, bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 23, da na’urar sadarwa, tare da wasu kayayyaki.
Rundunar ta ce nasarorin na nuna ci gaba da ƙoƙarin da dakarunta ke yi na tarwatsa hanyoyin sadarwa da ayyukan ’yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da suke gudanar da ayyukansu.
Ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da sa ido tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro game da duk wani motsi da suke zargi.