Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, lokacin da ya karɓi jakadan Denmark a Najeriya, Jens Ole Bach Hansen, tare da jami’in hulɗar tsaro na ƙasar, Laftanar Kanal Henrik Laugesen, a hedikwatar rundunar sojin da ke Abuja.
Shaibu ya ce haɗin gwiwar ƙasashen biyu na da muhimmanci wajen ƙarfafa ƙarfin rundunar soji, inganta dabarun gudanar da ayyukan yaƙi da kuma samar da kwanciyar
hankali a yankin, inda ya bayyana cewa musayar ƙwarewa da dabarun aiki za su taimaka wajen tunkarar sauye-sauyen ƙalubalen tsaro.
- Akpabio ya taya Oyebanji murna kan fara wa’adi na biyu a Ekiti
- Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance sabbin jami’an INEC gabanin zaɓe
Ya bayyana cewa fannoni da ake duba yiwuwar haɗin gwiwa a kansu sun haɗa da horar da sojoji kan dabarun yaƙi na zamani, kare jami’an tsaro, sa ido kan iyakoki, ilimin aikin soja da musayar ƙwarewa.
A cewarsa, waɗannan fannoni za su taimaka wajen inganta ayyukan soji musamman a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
A nasa ɓangaren, Jakadan Denmark, Jens Ole Bach Hansen, ya bayyana shirye-shiryen ƙasarsa na faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro da Najeriya, wanda a baya ya fi mayar da hankali kan harkokin tsaron teku a Tekun Guinea.
Ya ce Denmark na son haɗa kai kai tsaye da Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, musamman wajen horarwa, musayar ƙwarewar aiki da bunƙasa ƙarfin rundunar.
Jakadan ya kuma yaba wa juriyar sojojin Najeriya da nasarorin da suka samu a ayyukansu, tare da miƙa ta’aziyyarsa kan sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki.
Ya jaddada cewa Denmark na da niyyar ci gaba da haɗin gwiwar da zai amfani ƙasashen biyu wajen inganta tsaro da zaman lafiya, waɗanda ke da muhimmanci ga bunƙasar tattalin arziki da ci gaba mai ɗorewa.