Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance waɗanda ya naɗa a matsayin sabbin kwamishinonin ƙasa da kwamishinonin zaɓe na jihohi a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), bisa la’akari da babban zaɓen da ake sa ran gudanarwa a watan Janairu mai zuwa.
Tinubu ya miƙa sunayen sabbin kwamishinoni na ƙasa huɗu da kwamishinonin zaɓe na jihohi biyu domin cike guraben wasu jami’an hukumar da wa’adinsu ya kare.
Daga cikin waɗanda aka ambata akwai Farfesa Mustapha Aliu, wanda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru a matsayin wakilin Arewa maso Yamma, da Bashir Muhammed Umar, wanda zai maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu a matsayin wakilin Arewa ta Tsakiya.
- ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki kan kiran Atiku ya janye takara
- Akpabio ya taya Oyebanji murna kan fara wa’adi na biyu a Ekiti
Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya gabatar da sunan Misis Oluwatoyin Babalola, kwamishinar zaɓe ta jihar Osun, domin ta zama kwamishinar ƙasa mai wakiltar Kudu maso Yamma, yayin da Dakta Bala Bila, wakilin Arewa maso Gabas, zai ci gaba da aiki bayan sake naɗa shi.
A ɓangaren kwamishinonin zaɓe na jihohi, Tinubu ya naɗa Dakta Samuel Akinjide Akinleye domin wakiltar Jihar Ekiti, da Zahradden Basiru Sanusi daga Jihar Jigawa, wanda zai maye gurbin Farfesa Saidu Ahmed Babura.
Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 16 ga Oktoba, 2026, ta ce Majalisar Dattawa za ta tantance waɗanda aka naɗa kafin tabbatar da su.