An gudanar da horon ne a babban ɗakin taro da ke ginin fasaha na hedikwatar hukumar a Abuja, inda aka kammala shirin horaswar kan tsarin Border Control and Immigration Management System (BCIMS).
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyu, sun ƙwato bindigogi AK-47 huɗu a Sokoto
- Najeriya da Denmark za su ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da musayar bayanan sirri
Hukumar ta ce shirin na daga cikin ƙoƙarinta na amfani da fasaha wajen gudanar da ayyukan kula da iyakoki, tare da ƙara wa jami’an ƙwarewar fasaha da za ta taimaka musu wajen inganta tsaro.
Ta ƙara da cewa horon zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron iyakoki, inganta ayyukan leƙen asiri da kuma yaƙi da laifuffukan da suka shafi ƙasashe daban-daban.