Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe naira biliyan 10.96 domin gina rukunin hanyoyi 11 tare da magudanan ruwa a yankunan Arkilla Federal da Arkilla State Low-Cost da ke cikin birnin Sokoto.

Sanarwar da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar 17 ga Oktoba, 2026, ta ce an amince da kuɗin ne a taron Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na tara a shekarar 2026, wanda Gwamna Ahmed Aliyu ya jagoranta ranar Alhamis.

Majalisar ta kuma amince da kashe naira biliyan 8.54 domin gina babbar hanya mai titi biyu daga Tsehen Masu ta New City Kwasai zuwa tsohon titin saukar jiragen sama.

Haka kuma, ta ware naira biliyan 1.78 domin wasu ayyukan hanyoyi da suka haɗa da hanyoyin da suka haɗu da Kaduna Road da Tsafe Road, da hanyoyi a yankin Guiwa da kuma gyaran Bunza Road.

A ɓangaren samar da ruwa, majalisar ta amince da kashe naira biliyan 7.84 domin gina rijiyoyin burtsatse 200 masu amfani da hasken rana, waɗanda za su samar da ruwa ga yankunan da ke tsakanin birane da karkara a ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Ta kuma ware naira miliyan 249.4 domin sayen kayan haƙa rijiyoyi, da famfunan ruwa da sauran kayayyakin gyaran tsarin samar da ruwa a karkara.

A fannin lafiya, an amince da gyaran manyan asibitocin Tureta da Rabah kan kuɗin naira miliyan 377.9 da miliyan 302.8 bi da bi, tare da sake bayar da kwangila da kammala babban asibitin garin Dange kan naira miliyan 383.3.

Haka kuma, an amince da gyaran wasu cibiyoyin lafiya a Badon Barade da Alu Quarters da ke yankin Mana.

A ɓangaren ilimi, majalisar ta amince da gyaran zauren taro da ya lalace a Kwalejin Fasaha ta Umaru Ali Shinkafi kan naira miliyan 492.4, sayen kayan koyarwa da koyo ga Jami’ar Ilimi ta Shehu Shagari kan naira miliyan 99.9, da kuma gyaran Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Tambuwal kan naira miliyan 911.5.

Sanarwar ta kuma bayyana amincewa da ayyukan gyaran masallatai da kammala wasu gine-gine na addini, ciki har da ƙarin ayyukan kammala Masallacin Juma’a na Sultan Sa’ad Abubakar da ke Guiwa kan naira miliyan 694.7, da gyaran Masallacin Juma’a na Tangaza kan naira miliyan 243.1.

Majalisar ta kuma amince da wasu ayyukan gine-gine da sayen kayan aiki domin kare kadarorin gwamnati.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *