A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar, rundunar ta ce ci gaba da fitar da ruwa daga wurin ya taimaka wajen rage yawan ruwan sosai, kuma ana ƙoƙarin fitar da mafi yawan ruwan da ya rage, gwargwadon yanayin wurin.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana ƙarfafa ganuwar da ke kewaye da wurin ta hanyar amfani da buhunan yashi domin hana ta rushewa da kuma tabbatar da daidaiton wurin yayin da ake ci gaba da fitar da ruwan.
- ’Yan majalisar Zamfara takwas sun koma APC bayan ganawa da Tinubu
- Jihar Cross River ta jaddada aniyar yaƙi da ƙarancin abinci
Rundunar ta bayyana cewa aikin na buƙatar ci gaba da amfani da dabarun injiniya da fitar da ruwa a cikin yanayi mai wahala. Ta yaba wa jami’an da ke aikin da sauran hukumomin da ke taimakawa, musamman kamfanin Hitech Construction, bisa gudummawar da yake bayarwa.
Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya yaba wa tawagar aikin bisa jajircewa da ƙwarewarsu, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aikin cikin aminci da tsari, yayin da ake gudanar da bincike kan hatsarin jirgin.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da aikin tare da bayar da sahihan bayanai a kan lokaci, sannan ta gode wa al’ummar Igbokoda da sauran masu ruwa da tsaki bisa haƙuri da goyon bayan da suke bayarwa.