Gwamnatin Jihar Cross River ta sake jaddada aniyarta na yaƙi da ƙarancin abinci da samar da ingantaccen tsarin samar da abinci mai gina jiki, yayin bikin Ranar Abinci ta Duniya ta 2026 da aka gudanar a Calabar ranar 16 ga Oktoba.

Ma’aikatar Noma da Bunƙasa Ban-ruwa ta jihar ce ta shirya bikin tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Kiwo, da Bunƙasa Kamun Kifi, da sauran masu ruwa da tsaki a fannin noma. Taken bikin na bana shi ne, “Ƙirƙira a Yau, Samar da Abinci a Gobe.”

Kwamishinan Noma da Bunƙasa Ban-ruwa, Johnson Andiambey Ebokpo, wanda Babban Sakataren ma’aikatar, Dr Odey Joseph Ikongha, ya wakilta, ya ce taken bikin ya dace da buƙatar samar da sabbin hanyoyin magance ƙarancin abinci.

Ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Bassey Edet Otu na ƙoƙarin ƙara yawan amfanin gona, inganta damar manoma na samun muhimman kayan noma da kuma bunƙasa tsarin noma mai ɗorewa.

Ya bayyana wasu shirye-shiryen ma’aikatar, ciki har da shirin noman doya ta iri mai cibiyoyi 40 da al’ummomi ke jagoranta, da shirin noman wake mai cibiyoyin iri 12, da kuma shirin noman waken soya domin ƙara samar da abinci da bunƙasa tattalin arzikin manoma.

Ya kuma ambaci kafa cibiyoyin binciken noma a yankunan sanatoci uku na jihar, da shirye-shiryen ban-ruwa da za su taimaka wajen yin noma a duk tsawon shekara.

Ebokpo ya ƙara da cewa shirin bunƙasa noman kofi, koko, dabino da sauran amfanin gona masu muhimmanci na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin faɗaɗa samar da amfanin gona, ƙarfafa sarrafa shi da samar da guraben tattalin arziki ga al’ummomin karkara.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan Kiwo, da Bunƙasa Kamun Kifi, Francis Ekpenyong, wanda Glory E. Edet ta wakilta, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da wadatar abinci mai gina jiki.

Sauran waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da wakilan Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), da ƙungiyoyin manoma, da ƙungiyar mata masu aikin gona da sauran hukumomi da ke tallafa wa ci gaban noma.

An kuma duba kayayyakin da aka baje kolinsu, waɗanda suka nuna gudummawar manoma da masu sarrafa amfanin gona wajen samar da abinci, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

A jawabin godiya, Daraktar Abinci da Gina Jiki a Ma’aikatar Noma da Bunƙasa Ban-ruwa, Benedethe Ntiero Mgbe, ta yaba wa Gwamna Otu bisa samar da yanayin da ke tallafa wa ci gaban noma.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *