Baba-Ahmed ya yi tambaya kan abin da masu yaƙin neman sake zaɓen Tinubu da APC, musamman a jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto, Katsina, Borno, Yobe, Kwara, Kaduna, Plateau, Kogi da Nasarawa, za su gaya wa jama’a domin neman goyon bayansu.
- Jami’an tsaro sun kama mutane 430, ciki har da mata 50, a Yamai
- Hafsan Sojojin Najeriya ya isa Rwanda domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro
Ya yi zargin cewa masu yaƙin neman zaɓen za su raba kuɗaɗe masu yawa domin samun goyon bayan jama’a, amma ya ce hakan ba zai sa al’ummar Arewa su manta da abin da ya kira wulakanci da tozarta su a lokacin mulkin Tinubu ba.
Shugaban PRP ya bayyana cewa al’ummar Arewa za su nuna cewa su ma ’ya’yan ƙasa ne masu ’yancin zaɓen shugabannin da suke so, yana mai cewa idan suka ƙi goyon bayan APC da Tinubu, bai kamata wani ya yi ƙoƙarin sauya sakamakon zaɓensu ba.
Ya kuma yi kira ga masu goyon bayan Tinubu da APC da su ci gaba da fafutukar neman goyon baya idan sun ga dama, yana mai cewa jam’iyyarsa za ta tsaya kan matsayinta.