Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya isa birnin Kigali na ƙasar Rwanda domin ziyarar aiki ta kwanaki biyar da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen biyu da inganta tsaro a yankin Afirka.

Ziyarar, wadda za ta gudana daga ranar 18 zuwa 23 ga Oktoba, 2026, ta biyo bayan gayyatar da Hafsan Sojojin Ƙasa na Rundunar Tsaron Rwanda (RDF), Manjo Janar Vincent Nyakarundi, ya yi masa.

Nyakarundi ne ya tarbe shi tare da Mukaddashin Babban Kwamishinan Najeriya a Rwanda, Ambasada Ibrahim Zanna.

A yayin ziyarar, ana sa ran rundunonin sojojin ƙasashen biyu za su yi musayar ƙwarewa da gogewa kan ayyukan soji, tare da tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen yaƙi da ta’addanci da sauran sabbin barazanar tsaro.

Tattaunawar za ta kuma mayar da hankali kan samar da dabarun haɗin gwiwa domin tinkarar ƙalubalen tsaro da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Afirka.

Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin Laftanar Janar Shaibu na ƙarfafa dangantakar soji tsakanin ƙasashen Afirka, bunƙasa ƙwarewar rundunonin soji da inganta haɗin gwiwar tsaro, daidai da shirin sauye-sauyen da Rundunar Sojojin Najeriya ke aiwatarwa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *