Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce ta ceto mutane biyu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Gana da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, tare da kwato tumaki da awaki da aka sace.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar ranar 19 ga Oktoba, 2026, rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:42 na rana ranar 18 ga Oktoba, lokacin da ’yan bindiga masu yawa suka kai hari garin tare da harbe-harbe a sama, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.

Sanarwar ta ce maharan sun yi garkuwa da mutane biyu, sun kwashe babura shida, sannan suka sace wasu tumaki da awaki waɗanda ba a bayyana adadinsu ba.

Bayan samun rahoton harin, jami’in ’yan sanda na sashen Bukkuyum ya tattara jami’an rundunar ya tura su wurin, tare da jami’an tsaron al’umma (CPG) da ’yan sa-kai.

Haɗin gwiwar jami’an tsaron ya kai ga ceto mutanen biyu ba tare da sun samu rauni ba, da kwato dabbobin da aka sace da mayar da su ga masu su.

Sai dai rundunar ta ce jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ganowa tare da cafke waɗanda suka kai harin, waɗanda suka tsere, da kuma kwato baburan da suka sace.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP A. M. Bello, ya yaba wa jami’an tsaro da suka shiga aikin ceto cikin gaggawar da jajircewarsu.

Ya kuma sake tabbatar da aniyar rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira ga mazauna jihar da su riƙa bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙi da aikata laifuka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *