Kimanin ‘yan majalisar wakilai 13 ne suka sauya sheka bayan dawowar majalisar daga hutun makonni 4.
A zaman majalisar na ranar Talata, Shugaban Majalisar Tajuddeen Abbas ya karanto wasiku dake bayyana dalilan wakilan na sauya Shekar a gaban wakilan majalisar.
Daga cikin ‘wadanda suka sauya shekar akwai Honarabul Gaza Jonathan daga Jihar Nasarawa, na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da ya koma Labour Party (LP), sai Honarabul Alex Egbona daga Jihar Cross River, da ya tsallake All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP)
Sauran wakilan sun hadar da Honarabul Esosa Iyawe daga Jihar Edo, wanda ya bar (APC) zuwa National Democratic Congress (NDC)
Wakilan Jihar Katsina guda biyu da suka hadar da Honarabul Sani Lawal Uli Mai wakilitar Mazabun Baure da Zango, da Honarabul Shehu Dalhatu Tafoki Wakilin Faskari,Kankara da Sabuwa ne suka fice daga jam iyya mai mulki ta (APC) zuwa Jam’iyyar hamayya ta (PDP).
Wakilan Jihar Oyo kuwa guda Shida ne suka koma Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), da suka hadar da Honarabul Adebayo Adepoju, Adedeji Olajide, Ojo Akinola, Oyedeji Oyeshina, Oyekunle Folajimi, da Abass Adigun daga (PDP)
Daga Jihar Delta akwai Honarabul Etanabene Benedict da ya bar Labour Party (LP) zuwa PDP, sai wakilin Katagum ta jihar Bauchi Honarabul Auwalu Abdu Gwalabe da ya bar PDP zuwa (APM)
‘Yan majalisar sun bayyana cewa dalilan sauya shekar sun hada da matsaloli na cikin gida da rikicin shugabanci, da rarrabuwar kawuna a tsakanin tsofaffin yayan jam’iyyun, da ke zame musu tsaikon sauke nauyin Al’ummar da suka zabe su.
