Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce ta samu nasarori uku a cikin sa’o’i 24, ciki har da dakile fashi da makami, kama wanda ake zargi da kisan kai da kuma kama wata mata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

A samamen farko, jami’an ’yan sanda sun kama wani matashi mai shekara 22 a yankin Gidan Gona, kusa da Old Airport Road, Bauchi, bisa zargin tare ɗaliban sakandare uku da ke sanye da kayan makaranta, da yi musu barazanar soka musu wuƙa tare da kwace wayoyi biyu da darajarsu ta kai naira 50,000. \

A wani lamari kuma, ’yan sanda sun kama wani matashi mai shekara 20 bisa zargin kashe wani mutum mai suna Salim Moh’d ta hanyar soka masa wuƙa bayan wani saɓani a ranar 18 ga Oktoba, 2026.

Haka kuma, jami’an ’yan sanda sun kama wata mata mai shekara 28 a yankin Bayan Gari, Bauchi, bayan samun bayanan sirri.

Rundunar ta ce sun gano ƙananan buhuna guda 10 na busassun ganyayyaki da ake zargin wiwi ne, da kuma ɗan ƙaramin adadin Methamphetamine, wanda aka fi sani da Ice.

A sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar 20 ga Oktoba, 2026, rundunar ta ce za ta ci gaba da yaƙi da laifuffuka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *