Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gudanar da taron tattaunawa a birnin Beijing na China, domin duba hanyoyin sauƙaƙa biyan kuɗi da daidaita hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen biyu, tare da inganta kasuwanci da zuba jari.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya jagoranci taron na ranar 21 ga Oktoba, 2026, wanda ya haɗa ’yan kasuwa da shugabannin harkokin kuɗi da masana’antu da ke gudanar da ayyuka tsakanin Najeriya da China.
Taron ya bai wa mahalarta damar bayyana ƙalubalen da suke fuskanta wajen gudanar da kasuwanci a ƙasashen biyu, tare da tattauna hanyoyin inganta biyan kuɗi da daidaita hada-hadar kuɗaɗe ta ƙetare iyakoki.
- Atiku ya nemi Tinubu ya yi bayanin kan Naira biliyan 10 na yaƙi da Ebola
- Akpabio ya buƙaci Birtaniya ta ƙara zuba jari Najeriya
- Majalisar Wakilai ta nemi a koma kan asalin hanyar Lagos–Calabar
An kuma gabatar da jawabi mai taken “Najeriya na Ci Gaba: Sauye-sauye, Juriya da Shirye-shiryen Faɗaɗa Tattalin Arziki”, wanda ya bayyana manufofin sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya, ingantuwar wasu muhimman alamomin tattalin arziki da damar zuba jari.
CBN ya ce taron Beijing wani ɓangare ne na shirinsa na ƙarfafa haɗin gwiwar kuɗi a Asiya, bayan tattaunawar da aka yi a Singapore da kuma taron shekara-shekara na Asusun Ba da Lamuni na Duniya da Bankin Duniya a Bangkok.
Shirin ya mayar da hankali kan bunƙasa sabbin hanyoyin hada-hadar kuɗi, sauƙaƙa biyan kuɗi da ƙarfafa alaƙar kasuwanci tsakanin Najeriya da abokan hulɗarta na ƙasashen Asiya.