Kwamitin bincike kan mutuwar fursunoni a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a Minna, Jihar Neja, ya ba da shawarar biyan diyya ta Naira biliyan 1.4 ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma mutanen da suka tsira daga lamarin.

Rahoton ya bayyana cewa kwamitin karkashin shugabancin tsohun daraktan hukumar NSCD Jonathan Kure ya ba da shawarar biyan iyalan kowane mutum daga cikin mamatan 33 Naira miliyan 30, yayin da kowane mutum daga cikin 41 da suka tsira zai samu Naira miliyan 10.

Baya ga biyan diyyar, kwamitin ya bukaci gwamnati ta samar da tallafin karatu ga ’ya’yan waɗanda suka mutu, da kuma kulawar lafiya da taimakon zamantakewa da tunani ga waɗanda suka tsira da iyalan da lamarin ya shafa.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa gwamnatin tarayya ta gabatar da uzuri a hukumance ga waɗanda lamarin ya shafa, a matsayin wani ɓangare na matakan gyara da tallafa wa waɗanda suka yi asara.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *