Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya jaddada muhimmancin samun hangen nesa, tsare-tsaren ci gaba da shugabanci mai manufa domin tabbatar da bunƙasar Afirka a nan gaba.
Jonathan ya bayyana hakan ne a wajen buɗe taron Elevate Africa Convening 2026 da aka gudanar a Accra, Ghana, ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Ògíamẹ̀ Atúwàtse III, Olu na Warri.
Ya ce ƙasashe irin su Singapore da Indiya sun bayar da darussa masu muhimmanci ga Afirka, inda Singapore ta mayar da hankali kan cancanta, gaskiya da haɗa kan al’umma, yayin da Indiya ta zuba jari a jami’o’in bincike da bunƙasa kimiyya da fasaha.
- IMF ya naɗa ɗan China Min Liao a matsayin mataimakin manajan daraktansa
- Sojojin Nigeria sun dakile harin kwanton ɓauna a Zamfara, sun kwato dabbobi 520 a Sokoto
A cewarsa, ya kamata ƙasashen Afirka su zuba jari a ingantaccen ilimi da fasaha domin bai wa matasa ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen ƙirƙire-ƙirƙire, samar da arziki, bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi masu ɗorewa.
Game da batun biyan diyya kan illolin da Afirka ta fuskanta a tarihi da kuma rage nauyin basussuka, Jonathan ya buƙaci shugabannin nahiyar su yi aiki tare ta hannun Tarayyar Afirka domin samar da matsaya guda da za ta kare muradun nahiyar a tattaunawar ƙasa da ƙasa.
Ya ƙara da cewa ci gaban Afirka na buƙatar zuba jari mai ma’ana, haɗin gwiwar hukumomi da jajircewa wajen gina makomar al’ummarta, yana mai cewa haɗa murya kan muhimman batutuwan nahiyar zai taimaka wajen inganta tasirin Afirka a duniya.