Mambobin tawagar Najeriya da ke tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Makka sun yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa gwamnatinsa a matsayinsu daban-daban domin bunƙasa ƙasar da inganta rayuwar al’umma.
Sun bayyana hakan ne yayin wani liyafar cin abincin dare da suka yi tare da shugaban ƙasar a yammacin Lahadi a birnin Makka.
- Kwankwaso ya zargi wasu ’yan hamayya da ƙoƙarin cire sunan Gwarzo daga jerin ’yan takarar Kano
- ADC ta ce babu hujjar da za ta ɓoye gazawar Tinubu wajen samar da wutar lantarki
Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, da kuma ’yan kasuwa da masana’antu ƙarƙashin jagorancin Abdulsamad Rabiu na rukunin kamfanonin BUA.
Haka kuma, Ministocin Shari’a da Lafiya na cikin waɗanda suka halarci liyafar, inda suka tattauna batun ci gaba da haɗin kai wajen tallafa wa ƙasar.
A yayin taron, Shugaba Tinubu da sauran mahalarta sun jaddada muhimmancin yin addu’a domin samun Najeriya mai ci gaba da zaman lafiya.