Mai Bai wa Gwamnan Sokoto Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Faruk Labbo, ne ya bayyana hakan, inda ya ce matakan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa rayuwar matasa da samar musu da hanyoyin dogaro da kai.
- ADC ta ce babu gwamnan da ke da ikon hana jam’iyya gudanar da kamfen a jiha
- ’Yan sanda sun sanar da sauya hanyoyin zirga-zirga a Lafia gabanin gangamin APC
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na gudanar da shirye-shiryen koyar da sana’o’i domin bai wa matasa ƙwarewar da za ta taimaka musu wajen samun abin yi da inganta rayuwarsu.
Labbo ya ce waɗannan shirye-shirye na daga cikin dalilan da suka sa ƙungiyoyin matasa daban-daban suka shirya gangamin nuna godiya ga gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu bisa ƙoƙarinta na bunƙasa matasa.
A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan Sokoto, Alhaji Idris Mohammed Gobir, ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da suka shafi bukatun al’umma domin inganta rayuwarsu da bunƙasa tattalin arzikin jihar.