Rundunar ’yan sandan Najeriya ta yi gargaɗin cewa za ta kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen lalata fastoci, tutoci da allunan tallan ’yan takara a lokacin yaƙin neman zaɓen 2027.

Rundunar ta bayyana cewa ba za ta lamunci rashin haƙurin siyasa da lalata kayan yaƙin neman zaɓen abokan hamayya da gangan ba, inda ta ce waɗanda suka aikata laifin da kuma waɗanda suka ɗauki nauyin aikata shi za su fuskanci hukunci.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce cire fastocin wani ɗan takara ba bisa ƙa’ida ba ko lalata su laifi ne na ɓarna da dukiya, wanda doka ta tanadi hukunci a kansa, ciki har da Sashe na 451 na Dokar Laifuka da Sashe na 326 na Dokar Penal.

Saboda haka, Sufeto-Janar na ’yan sanda, Olatunji Disu, ya umarci kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja su ƙara sa ido, su gudanar da bincike kan rahotannin irin waɗannan laifuka tare da gurfanar da waɗanda ake zargi.

Umarnin ya kuma shafi ’yan siyasa da sauran mutanen da ke ɗaukar nauyi, ɗaukar ma’aikata ko ƙarfafa wasu su lalata kayan yaƙin neman zaɓen abokan hamayya, muddin bincike ya tabbatar da hannunsu a lamarin.

Rundunar ta jaddada cewa duk jam’iyyun siyasa da ’yan takara suna da haƙƙin samun kariya a ƙarƙashin doka, tare da kira gare su da magoya bayansu su mutunta ra’ayoyin juna, su bi ƙa’idojin yaƙin neman zaɓe, tare da tabbatar da zaman lafiya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *