Shugaban Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta NMDPRA, Rabiu Abdullahi Umar, ya bayyana cewa Najeriya na da damar jawo jarin dala biliyan 30 zuwa 50 kafin shekarar 2030 domin bunƙasa ɓangaren iskar gas.

Umar ya bayyana hakan ne yayin wani taron ƙasashen duniya kan makamashi na ADIPEC 2026, inda ya buƙaci masu zuba jari da masu samar da ababen more rayuwa daga sassan duniya su haɗa gwiwa da Najeriya wajen bunƙasa albarkatun iskar gas ɗinta.

Ya ce babban ƙalubalen Najeriya ba ƙarancin iskar gas ba ne, domin ƙasar na da tanadin iskar gas da ya kai tiriliyan 215.19 na cubic feet, sai dai matsalar ita ce rashin isassun ababen more rayuwa da za su kai iskar ga masana’antu.

Shugaban hukumar ya ce ayyukan bututun iskar gas na AKK da OB3, da kuma aikin ƙara ƙarfin bututun ELPS, sun kusa kammaluwa.

Ya ƙara da cewa gyaran doka na biyu kan tsarin jigilar iskar gas na Najeriya zai bai wa masu sayen iskar gas na masana’antu damar samun hidima cikin adalci da gaskiya.

Umar ya kuma bayyana cewa Asusun Samar da Ababen More Rayuwa na Iskar Gas a Tsakiya da Ƙasa (MDGIF) ya ware Naira biliyan 671 a matsayin hannun jari, matakin da ya jawo sama da dala biliyan ɗaya daga masu zuba jari masu zaman kansu domin aiwatar da ayyuka 31.

Ya ce Najeriya na da babbar dama ta bunƙasa tattalin arziki ta hanyar iskar gas, tare da gayyatar masu zuba jari da cibiyoyin samar da kuɗaɗe na duniya su haɗa gwiwa da ƙasar domin mayar da albarkatun iskar gas zuwa ci gaban tattalin arziki da zai amfani yankin baki ɗaya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *