Kwamandan bataliyar sojojin Senegal ta 10 (SENBATT 10) a rundunar wanzar da zaman lafiya ta ƙungiyar ECOWAS a Gambia (ECOMIG), Kanal Balla Moussa Mane, ya kai ziyarar farko ga dakarun Najeriya ta 11 da ke sansanin sojin da ke Yundum Barracks a Gambia.

Ziyarar ta gudana ne a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, inda Kanal Mane ya nuna godiyarsa ga kwamandan dakarun Najeriya, Laftanar Kanal Yahaya Mohammed Abdullahi, bisa kyakkyawar tarbar da shi da tawagarsa suka samu.

Kwamandan ya jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa da sadarwa tsakanin dakarun ƙasashe daban-daban da ke aikin, domin tabbatar da nasarar aikin ECOMIG da kuma samar da yanayin tsaro da zaman lafiya a ƙasar.

A nasa martanin, Laftanar Kanal Yahaya Mohammed Abdullahi ya yaba da ziyarar, tare da tabbatar da aniyar dakarun Najeriya ta ci gaba da haɗin gwiwa da sojojin Senegal da sauran rundunonin da ke aikin.

Ya kuma jaddada muhimmancin ƙara sa ido da inganta haɗin kai yayin da Gambia ke shirin gudanar da zaɓe mai zuwa.

Ziyarar ta ƙunshi bayanin halin da ake ciki, tattaunawa tsakanin kwamandojin, zagayawa sansanin dakarun Najeriya, musayar kyaututtuka da kuma ɗaukar hotunan haɗin gwiwa.

Hakan ya ƙara ƙarfafa dangantaka da haɗin gwiwar dakarun ƙasashen biyu wajen tabbatar da tsaro da cika manufofin rundunar ECOMIG.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *