Hukumar shige da fice ta ƙasar Gambia ta cafke mutum 198 da ake zargin suna shirin yin hijira ba bisa ƙa’ida ba a wasu samame da ta gudanar a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.
Hukumar ta ce ta cafke mutanen ne a yankunan North Bank da West Coast, ciki har da Faraba, Mandinaba, Batokunku, Wullinkama, Jokadou Darsilameh da Mayamba.
- NDLEA ta jaddada muhimmancin sa ido da wuri wajen yaƙi da shaye-shaye a rundunar sojin Najeriya
- Kwamandan sojojin Senegal ya gana da dakarun Najeriya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Gambia
Daga cikin waɗanda aka cafke akwai ’yan Gambia 79, ’yan Senegal 87, ’yan Guinea 14, ’yan Saliyo 13, ’yan Mali uku, ɗan Ghana ɗaya da kuma ɗan Madagascar ɗaya.
Hukumar ta bayyana cewa mutanen sun haɗa da maza 155 da mata 24, ciki har da ƙananan yara tara, maza shida da mata uku.
A halin yanzu, ana gudanar da bincike da tantance bayanansu a cibiyar hukumar da ke Tanji.
Hukumar ta ce samamen na daga cikin ƙoƙarinta na dakile hijira ba bisa ƙa’ida ba, ta hanyar ƙarfafa tsaron iyakoki da sintiri a cikin dare.