Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya da ba su karɓi katin zaɓensu na dindindin (PVC) ba, da su je su karɓa domin su samu damar kaɗa ƙuri’a a zaɓe.

Tinubu ya yi wannan kira ne yayin wani taro a Jihar Akwa Ibom, inda ya roƙi al’umma da su karɓi katunan domin kare makomarsu.

Shugaban ƙasar ya kuma yi alkawarin samar da ingantacciyar makoma, ci gaba, inganta ilimi, koyar da sana’o’i da samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *