Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya taya tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ‘yan ƙasa da shekara 17 ta Najeriya, Flamingos, murnar kai wa wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta 2026 da ake yi a Morocco.

Abbas ya bayyana hakan ne bayan da Flamingos ta doke Brazil da ci 3-1 a wasan kusa da na ƙarshe da suka fafata a ranar Laraba, inda ta samu damar karawa da Japan a wasan neman kambun gasar.

Shugaban ya buƙaci ’yan wasan da su ci gaba da nuna ladabi, jajircewa da ƙwazo, yana mai cewa ’yan Najeriya na fatan ganin tawagar ta dawo gida da kofin gasar.

Ya bayyana ’yan wasan da masu horar da su a matsayin jakadun ƙasar da suka cancanci yabo, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa matasan da ke da baiwar wasanni.

Wannan ne karon farko da Flamingos ta kai wasan ƙarshe na gasar, inda za ta fafata da Japan a ranar 7 ga Nuwamba, 2026.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *