Jami’an tsaro sun ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su, ciki har da wani matashin da ke bautar ƙasa (NYSC), bayan wani samame na haɗin gwiwa a Jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Samamen ya gudana ne a yankin Orita Fufu da ke Awa-Ijebu, a ƙaramar hukumar Ijebu North-East, inda jami’an tsaron suka yi nasarar kuɓutar da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su.

A yayin aikin, jami’an tsaron sun kashe mutum ɗaya da ake zargi da yin garkuwa da mutane, yayin da suka kama wani daban.

Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya yaba wa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ’yan sanda da jami’an tsaron Amotekun bisa nasarar aikin, musamman gudunmawar bayanan sirri da kayan aiki da DSS ta bayar.

Gwamnan ya kuma yaba wa ’yan sanda bisa gaggawar tura jami’ai zuwa wurin, yana mai gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin diddigin masu aikata laifukan da ke barazana ga tsaron al’umma.

Ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *