Mai magana da yawun kotun, Shuaibu Abdullahi, ya bayyana cewa kotun ta amince da hujjar cewa an shigar da ƙarar ne bayan wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada, don haka ta zama ƙarar da ta wuce lokacin sauraro.
- Shettima ya ce Tinubu ya kawo sauye-sauyen tsaro da ci gaba a Kudu maso Gabashin Najeriya
- NOA ta bayyana muhimman tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 gabanin zaɓen 2027
Kotun ta kuma duba zargin cika ƙuri’u fiye da kima da Maihaja ya gabatar, amma ta ce bai gabatar da hujjojin da za su tabbatar da zargin nasa ba.
Haka kuma, kotun ta gano saɓani da rashin daidaito a cikin bayanan shaidun da Maihaja ya gabatar, lamarin da ya sa ta bayyana shaidar tasu a matsayin wadda ba za a iya dogaro da ita wajen tabbatar da zargin ba.
Kotun ta ce ko da an shigar da ƙarar a cikin wa’adin da doka ta tanada, da har yanzu ba za ta yi nasara ba saboda gazawar Maihaja wajen tabbatar da zarge-zargen da ya gabatar.